Saudiyya za ta ba wa iyalan likitocin da suka mutu a bakin aikin kula da masu fama da cutar COVID-19 a kasarta.
Gwamnatin Saudiya ta amince a biya diyyar Riyal 500,000, kimanin Naira miliyan 61, ga ilayan kowanne daga likitocin.
- Ahmed Musa ya rabu da kungiyar AlNassr FC ta Saudiyya
- Saudiyya ta yi wa musulmi albishir kan aikin Umarah
- Budurwar Khashoggi ta maka Yariman Saudiyya a kotu
Iyalan likitoci akalla goma ne za su karbi diyyar kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana a ranar Talata.
Sanarwar ta ce za a ba da diyyar ce kan likitocin asibitocin gwamnati da masu zaman Kansu, ‘yan asalin Saudiya da ma ‘yan kasashen waje.
Ta ci gaba da cewa za kuma a bayar da irinsa kan ma’aikatan lafiya da jami’an tsaro da na farin kaya da annobar ta yi ajalinsu a bakin aikinsu.
Ta ce wadanda za a biya diyyarsu su ne wadanda aka sanar da gwamnati a hukumance cewa sun rasa rayukansu a bakin aiki.
Sanarwar ta yi bayani cewa gwamnatin kasar ta samu rahotan jami’an lafiya na farko da ya rasu a annobar a ranar 31 ga watan Maris, 2020.