Gwamnatin kasar Saudiyya ta fara biyan iyalan ma’aikatan lafiyar da cutar COVID-19 ta yi sanadiyyar mutuwarsu tallafin Riyal 500,000, kwatankwacin Naira miliyan 54.8.
Hakan dai wani bangare ne na aiwatar da shawarar Majalisar Ministocin kasar, kamar yadda Ministan Lafiyar kasar, Dokta Tawfiq Al-Rabiah ya sanar, inji kafar yada labaran kasar ta Saudi Gazette.
- Najeriya ta kammala gasar Olympics a mataki na 74
- Za a dawo da sufurin jiragen kasa daga Legas zuwa Kano a watan Agusta
Wadanda za su amfana da tallafin dai sun hada da iyalan ma’aikatan lafiya ’yan asalin kasar da kuma baki da ke aiki a kasar, ko dai jami’an tsaro ko kuma fararen hula masu aiki a asibitocin gwamnati ko na masu zaman kansu.
Ministan ya kuma ce kasar ta yanke shawarar bayar da tallafin ne la’akari da yadda mamatan, musamman ma’aikatan ko-ta-kwana suka sadaukar da rayuwarsu wajen yaki da annobar.
Ministan ya kuma yaba wa taimakon da Yarima Muhammad Bin Salman ya ke bayar wa wajen inganta lafiyar mazauna kasar, tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu sanadiyyar cutar.
Dokta Al-Rabiah ya kuma ce kasar ta cimma gagarumar nasara a yaki da cutar da kuma takaita yaduwarta ta kowacce fuska.
Taron Ministocin wanda ake gudanarwa a kowanne mako wanda aka yi ranar 27 ga watan Oktoban bara ne dai ya amince a fara biyan tallafin ga iyalan mamatan.
Za a fara biyan kudin ne tun daga wanda ya fara mutuwa ranar 31 ga watan Maris na bara, a lokacin da aka sami mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar.