A yammacin Asabar ne Ma’aikatar Cikin Gida ta Saudiyya, ta ba da umarnin sake bude filayen jiragen kasar, iyakokin kasa da na ruwa.
A ranar 20 ga Disambar 2020 ne Saudiyya ta rufe iyakokinta da kuma filayen jiragen sama, saboda sake bullar cutar cutar coronavirus a wasu kasashen Turai.
- Saudiyya na yi wa mutum 440,000 rigakafin coronavirus kyauta
- ’Ya’yan gidan Sarautar Saudiyya 150 sun kamu da Coronavirus
- Maniyyata Umrah za su fara isa Saudiyya ranar Lahadi
- Saudiyya za ta bude zirga-zirgar jirage ranar Talata
Dokar bude filin jirgin saman da iyakokin ta fara aiki ne a ranar Lahadi 3 ga Janairu 2021 bisa wasu sharuda da aka gindaya:
Duk bakon da zai shiga kasar daga kasar Birtaniya ko Afrika ta Kudu, to zai killace kansa na tsawon kwana 14.
Duk dan kasar da ya dawo daga tafiya, shi ma dole ya killace kansa a gida har tsawon mako biyu, sannan za a rika bincikar lafiyarsa a-kai-a-kai.
Matafiya daga kasashen da cutar ta sake bulla kuma dole ne su ma su killace kansu na kwana 7, za kum a yi musu gwajin cutar.
Matafiya da suka shigo kasar daga kasashen da cutar ba ta sake bulla ba kuma, za su killace kansu na tsawon kwana 3 kuma za a yi musu gwajin cutar.