A Birtaniya, Hukumar Dake Kula da Harkar Lafiyar kasar ta ce mutum bakwai daga cikin 30 din da suka fuskanci matsalar daskarewar jini bayan karbar allurar rigakafin COVID-19 ta AstraZeneca sun mutu.
Hakan dai na zuwa ne bayan kasashe da dama a Nahiyar Turai sun dakatar da ci gaba da amfani da rigakafin bayan matsalar ta daskarewar jinin da aka fuskanta.
- Kannywood: Ummi Zee-zee tana ‘yunkurin kashe kanta’
- Fallasa: Bidiyon yakin Syria ne Boko Haram ta yi wa kanikanci
Sama da allura miliyan 18 ce dai aka yi wa mutane a kasar kamar yadda gwamnatin kasar ta tabbatar a shafinta na intanet.
Sai dai ba a sami rahoton matsalar ta daskarewar jinin daga wadanda suka karbi rigakafin Pfizer da BioNTech ba yayin da ake ci gaba da bincike a kai.
To sai dai Hukumar Lafiya ta Tarayyar Turai ta tsaya kai da fata cewa amfanin rigakafin ya zarce illar da take dauke da ita, inda ta ce har yanzu babu wata cikakkiyar hujja da za ta iya alakanta matsalar da karbar rigakafin.
Sai dai lamarin ya sa kasashe da dama daukar matakin dakatar da ci gaba da amfani da allurar ko kuma takaita amfani da ita a kan tsofaffi saboda an gano yawanci matasa be suka fi fuskantar matsalar ta daskarewar jinin.
Ko a ranar Juma’a sai da kasar Netherlands ta sanar da dakatar da rigakafin ga ’yan kasa da shekaru 60 bayan an sami mutane biyar da suka fuskanci matsalar, inda mutum daya daga ciki ya mutu.
A kasar Jamus ma haka batun yake inda kasar ta dakatar da yin allurar ga ’yan kasa da shekaru 60 bayan mutum 31 wadanda yawancinsu matasa ne na can a kwance magashiyyan.
Ana sa ran dai nan da ranar bakwai ga watan Afrilun 2021 Hukumar Lafiyar Turai wacce a baya kamar takwararta Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da sahihancin allurar za ta sanar da sabon matsayinta kan rigakafin.