✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Sama da mutum 300 sun kamu a karo na farko a Najeriya

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa a karo na farko an samu mutum 381 da aka tabbatar sun…

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa a karo na farko an samu mutum 381 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus s cikin sa’o’i 24.

Da wannan sabon lissafin ne hukumar ta nuna cewa zuwa tsakar daren 7 ga watan Mayu, “mutum 3,526 ne aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.

Daga cikin wadannan mutum 381 da aka tabbatar sun kamu a baya-bayan nan dai, 183 a jihar Legas suke, sai 55 a Kano, 44 a Jigawa, 19 a Zamfara, 11 a Katsina, sai tara a Borno.

Akwai kuma takwas a jihar Kwara, bakwai a Kaduna, shida a Gombe, biyar a Ogun, hudu a Sakkwato, uku a jihohin Oyo da Rivers, biyu a Neja.

Sai jihohin Akwa Ibom, da Enugu da Plateau da ke da mutum guda guda da suka kamu.

Hukumar ta NCDC ta kara da cewa daga cikin adadin wadanda suka kamu an sallami mutum 601‬ bayan sun warke, yayin da mutum 107  suka riga mu gidan gaskiya.

Kididdigar da NCDC ta fitar ta nuna cewa adaddin sabbin kamuwa da cutar a Najeriya na kara hauhawa inda jihar Legas ke kan gaba, yayin da Kano ke biye mata da yawan wadanda suka kamu.