An samu raguwar sabbin wadanda suka kamu da COVID-19 a Najeriya idan aka kwatanta da adadin da aka fitar sa’o’i 24 baya.
Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa a ranar Asabtar an samu karin mutum 220 ne da aka tabbatar sun kamu da cutar – kwana guda kafin nan sabbin kamuwa 238 aka samu.
“Zuwa karfe 11.55 na daren 2 ga watan Mayu, mutum 2,388 ne jimilla aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya”, inji NCDC a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
- Coronavirus: Atiku ya bukaci a maida hankali a Kano
- Gwamnonin Arewa za su sayo motocin gwajin coronavirus
Daga cikin wadannan mutum 220 da aka tabbatar sun kamu a baya-bayan nan 62 a jihar Legas suke, sai 52 a Yankin Babban Birnin Tarayya, 31 a Kaduna, 13 a Sakkwato, 10 a Kebbi, tara a Yobe, shida a Borno, biyar a Edo da Bauchi, hudu a Oyo da Enugu da Gombe, da kuma uku a Zamfara.
Sai kuma jihohin Nasarawa, da Ebonyi, da Osun, da Plateau, da Kwara, da kuma Kano da ke da mutum biyu biyu da suka kamu.
Hukumar ta NCDC ta kara da cewa daga cikin wadanda suka kamu an sallami mutum 385 bayan sun warke, yayin da mutum 85 suka riga mu gidan gaskiya.
Wannan kididdiga da NCDC ta fitar ta nuna adadin sabbin wadanda aka tabbatar sun kamu ya ragu da mutum 18 cikin sa’o’i 24.
Hakazalika an samu raguwar sabbin wadada suka kamu a jihar Kano, inda aka samu karuwar mutum 2 kawai a cikin sa’a 24.