Jami’an gwamnati da ’yan majalisar wakilai takwas ne suka kamu da coronavirus a jihar Gombe.
Ranar Talata ne Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Alhaji El-Hassan Ibrahim Kwami, ya bayyana hakan, yana cewa kwamishinoni uku cikin 21 da ’yan majalisar dokoki biyar, ciki har da shugaban majalisar da mai bai wa gwamna shawara ne suka kamu da cutar.
Kwamishinan ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake karin haske kan yaki da cutar a Gombe, inda ya ce sakamakon gwajin da aka musu ne ya nuna suna dauke da wannan cutar kuma yanzu haka an killace su a wurare daban-daban.
Kwamishina Kwami ya kuma ce an nemi jami’an gwamnatin da su yi gwajin ne bayan mutuwar wani darakta da ke ofishin sakataren gwamnatin jihar, Shu’aibu Danlami, wanda ya rasu a sakamakon kamuwa da wannan cuta a makon da ya gabata.
Ya kuma nemi su ma ’yan jarida da su mika kansu don a yi musu gwajin tun da suna aiki tare da wadannan mutane kai tsaye musamman a irin wannan lokacin.
Sai dai ya ce Allah Ya kiyaye ba daya daga cikin mambobin kwamitin kar ta kwana masu yaki da annobar da aka gwada wanda ke dauke da wannan ita tun bayan mutuwar mataimakin sakataren kwamitin wanda bayan mutuwar sa ne aka gano cutar ce ta kashe shi.
Daga nan sai ya ce an umurci dukkan manyan daraktocin jihar da manyan sakatarori da su ma su je a gwada su don tabbatar da ko akwai wanda ya kamu a killace shi.