✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: Kwamishinan ’Yan Sandan Kuros Riba ya rasu

Kwamishinan ’Yan sanda na jihar Kuros Riba, Abdulkadir Lanre Jimoh ya rasu a safiyar ranar Juma’a bayan ya yi takaitacciyar jinya ta wasu ’yan makonni.…

Kwamishinan ’Yan sanda na jihar Kuros Riba, Abdulkadir Lanre Jimoh ya rasu a safiyar ranar Juma’a bayan ya yi takaitacciyar jinya ta wasu ’yan makonni.

Babban Daraktan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kalaba, Farfesa Ikpeme A. Ikpeme ne ya sanar da rasuwar kwamishinan bayan an gudanar da gwaje-gwaje da suka tabbatar da rasuwar mamacin a safiyar ranar Juma’a.

Daraktan bai bayyana musabbabin rasuwar ba amma an shawarci wadanda suka kusanci mamacin ko suka yi mu’amala tare da shi kafin rasuwarsa da su killace kansu har sai an yi musu gwajin cutar COVID-19.

Aminiya ta ruwaito cewa gabanin rasuwar Kwamishina Jimoh, jama’a da dama sun yi ido biyu da shi a zaben cike-gurbi da aka gudanar ranar 5 ga watan Disambar 2020 na mazabar Sanata mai wakiltar Arewacin Kuros Riba a Majalisar Dattawa.