Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yi mi’ara koma baya a kan umarnin da ta bayar tun da farko na sakin matar jagoran mabiya Shi’a, Sheik Ibrahim Zakzaky, wato Zeenat Zakzaky domin neman maganin COVID-19.
Tun da farko dai alkalin kotun, Mai Shari’a Gideon Kurada ne ya umarci a saki Zeenat kamar yadda lauyan dake kareta, Femi Falana ya bukata.
- Kotu ta ba da umarnin a kai matar Sheikh El-Zakzaky asibiti
- Kotu ta yi fatali da bukatar Sheikh Zakzaky
Falana dai a wancan lokacin ranar 26 ga watan Janairun 2020 ya gabatar da takardar likita da take bukatar a ba wacce yake karewa damar ta nemi lafiya a wajen gidan yari kamar yadda Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta tanada.
To sai dai kotun a hukuncin da ta yanke na ranar Alhamis ta soke wancan umarnin na farko bisa cewa wacce ake karewar ta sami lafiya.
Alkalin ya ce, “Lamarin ya sauya saboda wacce ake karewa ta sami cikakkiyar lafiya bayan samun kulawa daga asibitin gidan yarin dake Kaduna.
“Saboda haka, na bayar da umarnin jingine wancan hukuncin da na yi ranar 26 ga watan Janairu,” inji alkalin.
El-Zakzaky dai da matarsa Zeenat sun kasance a tsare tun shekarar 2015 bayan mabiyansa sun yi taho-mu-gama da sojoji a Zariya.
Yanzu haka dai malamin na fuskantar shari’a bisa zargin tayar da zaune tsaye, tara mutane ba bisa ka’ida ba da kuma muzgunawa jama’a.