Karin mutum 2,123 sun kamu da cutar COVID-19 a ranar Talata a Najeriya, wanda wannan shi ne mafi girman adadin wadanda suka kamu tun bayan bullar cutar a watan Fabrairun 2020.
Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), ya rawaito cewa adadin wadanda suka kamu ya haura da kashi 75 cikin 100 na wadanda aka samu a ranar Talata, 1368.
- Mutum 1 ya rasu, 70 sun bace bayan ruftawar wurin hakar ma’adinai a Myanmar
- Ba za mu karbi tubar ’yan bindiga ba, kashe su za mu yi —El-Rufai
Wannan shi ne karo na farko da Najeriya ta samu adadi mafi yawa na wadanda suka harbu da cutar cikin rana guda.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da Legas a matsayin jihar da ta fi kowace adadi mai yawa, inda ta ke da mutum 1,552.
Sai birnin tarayya da ke da mutum 197, Edo na da mutum 155, Ribas 81, Delta 44, Filato 33.
Sauran jihohin su ne Kwara 30, Kano 16, Enugu 12, Gombe na da biyu, sai Jihar Bauci mai mutum daya.
NCDC ta ce adadin masu cutar a ranar Laraba ya kai mutum 12,547 baki daya a fadin Najeriya.
Wannan na nuni da samun karin mutum 3,039 da suka kamu da cutar idan aka kwatanta da mutum 9,508 da suka harbu a baya.
Kazalika, mutum hudu sun mutu sakamakon kamuwa da COVID-19, wanda ya da yawan wadanda suka mutu ya karu zuwa 2,989.
Adadin wadanda suka kamu da cutar a ranar Laraba ya nuna zuwa Najeriya na da mutum 227,378 da suka kamu, da 211,761 da suka warke.