Gwamnonin jihohin Najeriya 36 za su yi taro ranar Laraba don tattaunawa a kan dokar zaman gida da kuma nazari a kan ko ‘yan kasa na cin gajiyar tallafin rage radadin coronavirus.
Ana kuma sa rai gwamnonin za su tattauna a kan kudurin dokar Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na 2020 sannan kuma su yi duba na tsanaki a kan tsarin tattalin arzikin kasa bayan annobar COVID-19.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta bakin mai magana da yawunta, Abdulrazaque Bello-Barkindo, Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce wannan taron da za a gudanar kai-tsaye ta bidiyo shi ne zai kasance irinsa na takwas tun bayan barkewar annobar.
Hakazalika, sanarwar ta ce taron zai yi nazari a kan halin da ake ciki a jihohi daban-daban da kuma nemo nagartattun hanyoyin farfadowa daga mummunan tasirin annobar.
- COVID-19: Gwamnonin Najeriya sun kuduri aniyar rufe jihohi
- Coronavirus: Shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya ya killace kansa
Bello-Barkindo ya ce a sakon gayyatar da Babban Daraktan kungiyar, Mista Asishana Bayo Okauru, ya aike wa gwamnonin, an lissafo batutuwan da taron zai mayar da hankali a kai wadanda suka hada da sauraron bayanai daga kwamitin kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar, da wani sabon shiri na bayar da gudunmawa a karkashin Gamayyar Manyan ‘Yan Kasuwa (CACOVID), da kuma batun ma’aikatan lafiya masu aikin sa kai tare da duba yiwuwar ba su horo.
Ya ce taron, wanda aka tsara zai gudana da karfe 2.00 na rana zai kuma duba batun rarraba tallafin rage radadin matakan hana coronavirus yaduwa, daga bisani kuma ya karbi bayanai daga jihohin a kan yadda aikin yake gudana.
Sanarwar ta kara da cewa ana sa rai shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC), Mele Kyari, shi ma zai kasance a taron don yin bayani a kan irin gudunmawar da kamfanin yake bayarwa wajen yaki da cutar tun lokacin da aka samu barkewarta a Najeriya.