Gwamnnatin jihar Filato ta dada sassauta dokar da ta kafa ta hana fita zuwa daren Litinin maimakon daren Lahadi, kamar yadda ta sanar tun da farko.
Wata sanarwa da ke dauke da sa-hannun daraktan yada labaran gwamnan jihar, Dokta Makut Simon Macham, ta bayyana haka.
Sanarwar ta ce gwamnatin ta dada sassauta dokar ne saboda koke-koken da jama’ar jihar suka yi cewa Juma’a ranar hutun ma’aikata ce, don haka ba su samu damar fitar da kudade daga bankuna da sayen kayayyakin abinci ba.
Sanarwar ta kuma ce gwamnatin ta dada sassauta dokar ne don ta bai wa jama’a dama su je su cire kudade a bankuna kuma su sayi kayayyakin abinci, kafin daren Litinin dokar ta ci gaba.
Filato dai na cikin jihohin da suka ayyana dokar hana fita kwata-kwata da nufin hana cutar coronavirus yaduwa.
Zuwa daren Juma’a dai alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa mai dauke da cutar daya kawai aka samu a jihar ta Filato.