Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya warke daga cutar coronavirus bayan ya kwashe makwanni kusan hudu yana jinya.
Gwamnan ne ya sanar da warkewar tasa a shafinsa na Twitter, inda ya ce, “a yanzu na kammala warwarewa bayan sakamakon gwaji har biyu a jere ya nuna ba ni da [cutar]”.
Ya kuma jinjina wa iyalansa “wadanda ba damuwar yiwuwar rasa daya daga cikinsu kadai suka shiga ba, har ma da hadarin kamuwa su kansu”.
Malam Nasir El-Rufai ya kuma ce ransa ya yi fari da ganin kwazon da Kwamitin Cika Aiki a Kan Cutar COVID-19 na jihar Kaduna ya nuna wajen hana cutar yaduwa.
Gwamnan, wanda ya wallafa wasu hotuna da ke nuna alamun ya kwana biyu bai yi gyaran fuska ba, ya kuma yaba wa jami’an Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna da Asibitin Barau Dikko “saboda yadda suka nuna kwarewa da hazaka wajen jinyata”.
A karshen watan jiya ne dai gwamnan na jihar Kaduna ya saki wani bidiyo wanda a ciki yake bayyana cewa sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna ya kamu da cutar coronavirus.
Mataimakiyarsa Dokta Hadiza Balarabe ce ta rike ragamar mulkin jihar a tsawon makwannin da gwamnan ya yi a killace.