✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: Gidauniyar TY Danjuma ta raba tallafin N107m a Neja

Jihar Neja ta samu tallafin kayan abinci da na kariyar COVID-19 na Naira miliyan 107

Gwamnatin Jihar Niger ta karbi kayan tallafi na miliyan N107. 9 daga asusun karta kwana na tallafin COVID-19. 

Tallafin ya hada da kayan abinci da na kariya daga cutar wadanda mabukata da magidanta 25,000 za su amfana a fadin jihar.

Asusun da ke karkashin Gidauniyar TY Danjuma ne ya kaddamar da rabon kayan karkashin shugabanta, Janar Theophilus Yakubu Danjuma.

Gidauniyar ta samar da kayan tallafin ne da nufin ba wa mabukata da ‘yan gudun hijira da hukumomin da ke yaki da yaduwar COVID-19.

Kayan da aka raba a jihar ta Neja sun hada da buhunan shinkafa, masara, wake da gishiri guda 5,272 da kuma jarkokin man girki 5000.

Akwai kuma takunkumi 30,000, sinadarin tsaftace hanu 1,174, safar hannu 1,174, rigunan kariya 1,174, da takalman kariya 1,174.

Shugabar asusun tallafin COVID-19 a jihar, Toyosi Akerele ta ce an rarraba kayan ne ta karkashin kungiyar yaki da cutar, VSF COVID-19.

Ta ce an ba gwamnatin jihar rabin kayan abincin da aka raba, rabi kuma aka ba kungiyoyin sa kai, ‘yan gudun hijira, masu rauni da mabukata.

Toyosi ta ce rabon tallafin karo na uku zai gudana ne kai tsaye ga mabukata 204,330 a jihohin Kano, Kastina, Zamfara, Kaduna, Neja, Filato da Abuja.

%d bloggers like this: