Dakunan binciken da ke iya gwajin cutar coronavirus a Najeriya sun zama 13.
Hakan ya biyo bayan bude wasu karin cibiyoyin gwajin biyu ne a biranen Kaduna da Maiduguri.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta sanar da hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
“An kaddamar da sabbin dakunan bincike don gwajin #COVID-19 a DNA Lab, wani dakin bincike mai zaman kansa a Kaduna, da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri”, inji sanarwar.
- COVID-19: ‘Adadin gwajin da ake yi bai isa ba’
- COVID-19 a Daura: Yadda aka yi musayar zafafan kalamai
Hukumar ta NCDC ta kuma ce ana ci gaba da aiki a kan wasu cibiyoyin binciken a Sakkwato da Fatakwal.
Da ma dai akwai cibiyoyin gwaji uku a jihar Legas, biyu a Yankin Babban Birnin Tarayya, da dai-dai a jihohin Edo, da Oyo, da Osun, da Ebonyi, da Kano, da kuma Filato.
Masana da masu ruwa da tsaki dai sun sha bayyana cewa cibiyoyin gwajin sun yi kadan, kuma adadin gwajin da ake yi bai isa ba.
Wasu ’yan Najeriya dai suna ta kiraye-kiraye cewa a bude kofar gwajin ga kowa a matsayin hanya mafi sauki kuma mafi sauri ta taka wa annobar birki a maimakon ajin mutane uku kadai da NCDC ta ayyana.