✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Covid-19: Buhari ya yi wa Trump fatan samun sauki

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, fatan samun sauki bayan kamuwarsa cutar coronavirus. A sakon da ya wallafa kan…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, fatan samun sauki bayan kamuwarsa cutar coronavirus.

A sakon da ya wallafa kan shafinsa na Twitter, Shugaban Kasar ya yi fatan samun waraka ga Mista Trump da mai dakinsa, Melania Trump yana cewa wannan ya nuna hadarin da cutar take da shi a duniya baki daya.

 “Ina yi wa Shugaban Amurka, Donald Trump, da matarsa, Melania, fatan samun sauki cikin gaggawa daga cutar COVID-19”, inji Buhari.

Sanarwar da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasar, Mallam Garba Shehu ya fitar, ta ce faruwar hakan ya nuna irin barazanar cutar da kuma bukatar kawar da ita cikin gaggawa.

Garba Shehu ya ce, Buhari ya sake jaddada bukatar shawarwarin mahukuntan lafiya domin yaki da cutar.