Shugaba Muhammadu Buhari ya roki ’yan Najeriya su yi hakuri su ci gaba da zaman gida duk da matsi da takurar da hakan ke haifar masu.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mataimakinsa na musamman a kan harkar sadarwa da yada labarai, Malam Garba Shehu.
“Mun fahimci cewa a yau akwai ’ya’ya da babu dama su ziyarci iyayensu, da dattawan da aka raba da matasansu”, inji Shugaba Buhari, wanda ya kara da cewa, “Akwai kuma wadanda ke rayuwa irin ta hannu-baka-hannu-kwarya, wadanda sai sun fita suke samun na abinci, wadanda kuma suke fuskantar tsanani na zahiri”.
- Buhari ya ba da umarnin hana fita a Abuja da Legas
- COVID-19: ‘Gazawar’ Buhari wajen daukar mataki ta haifar da matsala
Sanarwar ta kara da ambato Shugaba Buhari yana cewa babu wata zababbiyar gwamnati da za ta nemi wadanda suka zabe ta su yi fiye da abin da gwamnatinsa ta ke nema al’ummar Najeriya su yi.
“Amma wajibi ne mu sake bukatar ku da ku ci gaba da martaba umarnin takaita zirga-zirga a inda aka bayar da shi, ku kuma yi biyayya ga kiraye-kirayen masana kimiyyarmu da jami’an lafiya: ku zauna a gida, ku wanke hannuwanku, ku ceci rayuka”, inji Buhari.
Sai dai shugaban kasar bai fito karara ya bayyana makomar dokar da aka ayyana ta hana fita kwatakwata a Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun ba—shin za ta zo karshe bayan mako biyu kamar yadda ya ba da umarni tun farko, ko za a tsawaita ta?
A maimakon haka, sai shugaban kasar ya ce a saurari abin da masana za su ce.
“Matakin sarayar da ’yancinku da muke nema ku dauka a yau ba zai zo karshe ba a tsawon lokacin da masu ba mu shawara ta fuskar kimiyya ke ganin ya zama wajibi”, a cewar shi.
Sanarwar ta kuma ce a yunkurinta na saukaka wa marasa karfi wahalhalun da zaman gida ka iya haifarwa, gwamnati ta dauki matakai.
“Ga wadanda suke shan bakar wahala, gwamnati ta sanar da daukar matakai da dama don taimakawa: za a fitar da tan 70,000 na hatsi daga Rumbun Adana Hatsi na Kasa don rabawa ga wadanda suka fi bukata, da raba wasu ’yan kudade da gwamnatin tarayya ta fara kuma a ci gaba da yi a jihohi da kananan hukumomi”.
Wasu gwamnatocin jihohi da ’yan siyasa da masu hannu da shuni na ta rarraba tallafin kayan abinci ga marasa karfi—amma a inda ake raba tallafin gwamanti akwai korafin cewa abin da ake bayarwa bai taka kara ya karya ba, ko kuma wasu na sama da fadi da kayan.
Sanarwar dai ta ce Shugaba Buhari ya fadi wadannan kalamai ne don ’yan Najeriya su san gaskiyar abin da ake ciki.
“A wannan lokaci mawuyaci hakkinmu ne mu fada maku gaskiya ba boye-boye… kasashe da yankunan duniya 210 ne ke fama da wannan annoba, don haka ba wanda za mu sa rai ya kawo mana dauki, babu wanda zai yakar mana wannan ita”.
Wadannan kalamai na Shugaba Buhari suna zuwa ne a daidai lokacin da wasu jihohin kasar ke sassauta dokokin da suka ayyana na takaita fita ko tarukan jama’a, matakin da masana suka ce yana da hadari matuka.