Wata kungiyar manyan ’yan kasuwa a Najeriya da ke tallafawa a yakin da ake yi cutar coronavirus, Gamayyar Yaki da Annobar COVID-19 (CACOVID), ta damka wata cibiyar killace masu dauke da cutar mai gadaje 66 ga gwamnatin jihar Kano.
An kafa gamayyar ta CACOVID ne bisa jagorancin attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, don tallafa wa yunkurin gwamnatoci a matakai daban-daban bayan bullar cutar a Najeriya.
Da yake jawabi yayin bikin mika cibiyar, wakilin gamayyar, Alhaji Abdulkadir Sidi, ya ce gidauniyar ta kashe sama da Naira miliyan 200 wajen daga likkafar cibiyar zuwa ta zamani.
Alhaji Sidi ya kara da cewa kayan aikin da gidauniyar ta samar a cibiyar daidai suke da na kowacce irinta a fadin duniya.
Ya kuma ce gudunmawar kari ce a kan sabuwar cibiyar killace masu cutar a filin wasanni na Sani Abacha mai gadaje 300 wacce ita ma za su danka wa gwamnatin jihar nan ba da jimawa ba.
“Gamayyarmu ta kashe sama da Naira miliyan 200 wajen gyarawa da samar da kayan aiki ga cibiyar killace masu cutar ta Abubakar Imam da ta tasamma durkushewa, wannan yana daga cikin irin hobbasar da muke yi wajen tallafa wa gwamnatoci wajen yaki da coronavirus a Najeriya”, inji Sidi.
A yayin da yake karbar cibiyar a madadin gwamnati da al’ummar jihar, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana godiyarsa ga gamayyar.
Ya ce al’ummar jihar Kano na matukar godiya ga Alhaji Aliko Dangote saboda tallafa wa jihar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.