Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya ta Jihar Filato (SUBEB) ta sanar da ranar 1 ga Fabrairu, 2021 a matsayin ranar da za a sake bude makarantun Firamare na gwamnati a fadin jihar.
Shugaban hukumar, Farfesa Mathew Sule ne ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) haka ranar Asabar a garin Jos.
- ’Yan sanda sun kashe masu satar mutane 2 a Filato
- Lalong ya bude makarantun Filato
- An yi sama da fadi da tallafin noman shinkafa a Filato
- Dubun mai yi wa kananan yara fyade a Filato ta cika
Farfesa Mathew ya ce, “Bayan umarnin da muka samu, ina kira ga Mukaddashin Sakataren Kananan Hukumomi 17, da muke da su, da su aiki tare da shugannin makarantu wajen dawo da yara makarantu.
“Shugabannin makarantu da malamai su tabbatar da tsaftar dalibai, don samun kariya daga COVID-19.
“Malamai su tabbatar da cewar an kammala zangon karatu na uku, tare da yin jarrabawa ga daliban kafin fara wani sabon zangon karatu,” cewar Farfesa Mathew.
Daga nan sai shugaban hukumar ya yi gargadin cewa dole ne a bude wa malaman makarantu sabuwar rajista, don tabbatar da suna zuwa aiki akan lokaci.