Adadin mutanen da aka sallama bayan sun warke daga wuraren da ake killace majinyata COVID-19 a Najeriya ya kai 2,007 zuwa yanzu.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta bayyana hakan a alakluma na baya-bayan nan da ta fitar, wadanda suka nuna mutum 221 suka riga mu gidan gaskiya.
Hakan na nufin a yanzu akwai mutum 5,033 da ke jinya a fadin kasar.
Hukumar ta kuma ce yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya ya kai 7,261.
Adadin ya kai haka ne dai bayan da aka samu sabbin majinyata 245 ranar Juma’a.
A cewar hukumar NCDC, 131 daga cikin sabbin majinyatan a jihar Legas suke, 16 a jihar Jigawa, 13 a Ogun, sai 12 a Borno.
Yayin da jihohin Kaduna da Oyo da Ribas da Ebonyi ke da mutum tara ko wacce, jihar Kano na da mutum takwas, Kwara na kuma mutum bakwai.
Sauran jihohin da aka samu sabbin kamu su ne Katsina mai mutum biyar, Akwai-Ibom da Sakkwato na da uku-uku, Bauchi da Yobe na da bibbiyu.
Jihohin Anambra da Gombe da Neja da Ondo da Filato da Bayelsa da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya na da mutum dai-dai ko wannen su.
Da wannan sabuwar kididdiga dai jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Legas ya kai 3,224 yayin da na Kano da na Yankin Babban Birnin Tarayya suka tashi 883 da 447 daki-daki.