Gwamnatin Jihar Anambra ta da dawo da dokar hana fita a jihar, wadda za ta fara aiki daga ranar Litinin 8 ga Fabrairu 2021.
Sanarwar na kunshe ne cikin wani jawabi da Sakataren Gwamnatin Jihar, Solo Chukwulobelu, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.
- Abin da ’yan bindigar Zamfara suka fada min —Sheikh Gumi
- Abduljabbar: Kotu ta ba da izinin hana shi wa’azi da rufe masallacinsa
- Za mu shiga yajin aikin har sai abinda hali ya yi ranar Juma’a — Ma’aikatan Jami’a
- ’Yan bindiga sun kashe karamar yarinya da iyayenta
“Gwamna Willie Obiano ya umarci ma’aikata daga mataki na 12 zuwa kasa da su ci gaba da aiki daga gida.
“Gwamnatin jihar nan na ci gaba da tabbatar da mutane na bin matakan kariyar COVID-19.
“Gwamnati ta kafa kotun tafi-da-gidanka, a fadin jihar don hukunta masu karya dokokin cutar coronavirus da aka shimfida,” inji Chukwulobelu.
Sai dai a wannan karon, Sakataren Gwamnatin jihar ya ce dokar kullen za ta fara aiki ne daga karfe 9 na dare zuwa karfe 6 na safe, a kullum.
Sannan an kafa kwamitin hadin gwiwa daga Ma’aikatar Lafiya da Ma’aikatar Kasuwanci, don zagawa cikin kasuwanni tare da sanya ido kan yadda jama’a za su ke bin matakan kariyar cutar.