Gwamnatin jihar Legas ta sanar da ranar 18 ga watan Janairun 2021 a matsayin ranar sake bude makarantun jihar don ci gaba da zangon karatu na 2020/2021.
Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Misis Folasade Adefisayo ce ta bayyana hakan ranar Litinin, inda ta ce za a sake bude su ne cikin matakan kariya da Gwamnatin Tarayya ta shimfida.
- An umarci Ma’aikatan Legas su ci gaba da aiki daga gida saboda Coronavirus
- Gwamnan Legas, Sanwo-Olu ya kamu da COVID-19
A watan Disambar 2020, gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya ba da umarnin sake rufe makarantun saboda sake bullar cutar COVID-19 a karo na biyu.
Kwamishiniyar ilimin ta kuma jaddada muhimmancin bin matakan kariya, don tafiyar da makarantun yadda ya dace.
Misis Folasade ta kuma shawarci makarantun kan yadda za su samar da tsarin yi wa dalibai bitar karatu daga gida, musamman ga wadanda ba su da lafiya ko wadanda suka kamu da COVID-19.
Sannan ta ce dole ne ga dalibai, malamai, masu ziyara su rika amfani da takunkumin rufe fuska, sannan a samar da wajen wanke hannuwa da kuma tabbatar da tsaftar makarantun.