Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya kuma shugaban kwamitin yaki da coronavirus, Boss Mustapha, ya jaddada cewa matakan yaki da cutar da za su zo nan gaba a kasar suna da matukar tsauri, sannan ya bukaci al’umma da su kare kansu.
Ya ce matakan kariya daga cutar za su fi karkata ne ga kula da kai “kuma kowanne a cikinmu dole ne ya dauki alhakin kare kansa da kansa”
Ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da kwamitin ke gabatar da jawabin da ya saba gabatarwa ga ‘yan kasar.
“Ya kamata a kula da shawarwarin da hukumomin kiwon lafiya suka bayar na ba da tazara tsakanin jama’a, tsaftar jiki, sanya kyallen rufe fuska, janye tafiye-tafiye da ziyara da ba su zama dole ba saboda duk abin da zai faru da mu zai dogara da abin da muke yi.
“Kokarin gwamnati a kullum shi ne ta samar da makatan kariya da kuma duk kayayyakin da ake bukata saboda dakile cutar ta coronavirus.
“Yadda ‘yan kasa ke daukar yanayin shi zai tabbatar da cewa za mu yi nasara ko akasin haka.
“Wannan shi ne gundarin batun; wannan shi ne mataki na gaba kuma alhaki ne a kan dukkaninmu”, inji Boss Mustapha.
Ya ce annobar ta yi gagarumar sauyi a kan yadda al’umma ke gudanar da harkokinsu inda ya nemi jama’a su yi kokarin daidaita lamarin.
Ya kara da cewa gwamnati za ta janye dokar kulle ne domin harkoki su dawo a hankali.
“Janye dokar dai bai nuna cewa annobar ta kare ba. Har yanzu cutar tana da hadari kuma ta ci gaba da barazana.
“Dole ne mu ci gaba da kulawa da taka tsan-tsan. Dole ne mu dauki alhakin abubuwan da muke yi.
“Dole ne mu dauki mataki na bai-daya don mu yi nasara a kan coronavirus”,
Mustapha ya ce jami’an tsaro za su ci gaba da tabbatar da dokar hana yawace-yawace ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da biyayya wa dokar.
Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce har yanzu ba a sanya wata rana da makarantu za su koma aiki a kasar ba duk da sassauta dokar kulle da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a Babban Birnin Tarayya da kuma johohin Legas da Ogun.
“Gwamnatin tarayya ba ta shirya sanya rayukan yara a cikin hadari ba saboda bude makarantu.
“Shugaban kasa ya bayyana yadda za a bude harkoki a hankali amma ba na tunanin ya dace mu ba da ranar dawowar makarantun a yanzu. Ba ma son mu sa yara cikin hadari.
“Babu makarantar da za ta iya aiki ba tare da al’umma ba.
“Akan batun chanjin ajin karatu, za a yi jarabawa ne yayin da muka tabbatar dalibai sun fahimci abubuwan da za su ba su damar shiga aji na gaba. Wadanda suke shirin gamawa kuma muna kokarin shirya su kuma za mu ci gaba.
“Za mu ci gaba da hakan har sai mun tabbata sun shirya tsaf saboda jarabawar. Hukumar jarabawa ta WAEC ba ta soke jarabawar ba. An dage ta ne saboda a shirya sosai.”
Shi kuwa ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, cewa ya yi Shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna ta waya da shugaban kasar Amurka Donald Trump, wanda ya yi alkawarin taimaka wa Najeriya da na’urar nunfashi don ta yaki cutar coronavirus.