Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCTA) ta rusa gidajen sharholiya guda biyar da wani gidan dambe saboda karya dokokin kariyar cutar COVID-19.
Kwamitin Kar-ta-kwana da Ministan Abuja ya kafa, wanda shi ne ya rushe gidajen a unguwannin Daki Biyu da Gwarimpa ya kuma kama mutum 25 saboda karya dokokin a fadin Abuja.
- Jami’ar ABU Zariya ta sanar da ranar komawar dalibai
- Ma’aikatan jami’o’in Najeriya za su shiga yajin aikin sai Baba ta gani
Jami’an tsaro na ’yan sanda, ’yan sandan farin kaya (SSS) da kuma rundunar tsaro ta NSCDC ne suka yi wa tawagar rakiya yayin aikin.
Da yake jawabi ga ’yan jarida yayin gudanar da aikin, kakakin kwamitin, Ikharo Attah ya ce sun sha jan kunnen masu gidajen a kan karya dokokin kariyar cutar amma suka yi kunnen kashi.
“Dubban mutane na taruwa a wadannan kananan wuraren shakatawar domin kallon ’yan dambe da masu rawar gala da wasan kwaikwayo.
“Mun lura a daya daga cikin gidajen babu wani abu mai suna kyallen rufe fuska, bayar da tazara ko tsaftace hannuwa,” inji Mista Ikharo.
Sai dai ya gargadi jaruman Masana’antar Fina-finai ta Kannywood da ke zuwa irin wadannan wuraren da su kauce wa yin hakan.
“Idan muka kama su, ba ruwanmu da sunansu ko daukakarsu, za mu kama su mu gurfanar da su a gaban kuliya,” inji shi.