A karo na biyu a jere, adadin mutanen aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya haura 300.
Kididdiga ta baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta najeriya (NCDC) ta wallafa sun nuna cewa a tsakanin tsakar daren 7 ga watan Mayu da tsakar daren 8 ga wata, an tabbatar da mutum 386, adadin da ya zarta na kwana guda kafin nan da mutum biyar.
Alkaluman na hukumar NCDC dai sun nuna cewa jimilla mutum 2,912 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya zuwa yanzu.
Daga cikin wannan adadi kuwa, mutum 117 sun riga mu gidan gaskiya, yayin da aka sallami mutum 679 bayan sun warke.
Mutum 176 daga cikin sabbin kamun, kamar yadda alkaluman suka nuna, a jihar Legas suke, 65 a Kano, 31 a Katsina, 20 a Yankin Babban Birnin Tarayya.
Sai kuma jihar Borno mai mutum 17, Bauchi mai 15, Nasarawa mai 14, Ogun mai 13, da Filato mai 10.
Jihohin Oyo da Sakkwato da Ribas kuwa na da mutum hurhudu yayin da Kaduna ke da uku, Edo da Ebonyi da Ondo ke da bibbiyu, Enugu da Imo da Gombe da Osun kuma mutum daya ko wacce.