✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: Yawan wadanda suka kamu ya kai 111

Hukumar Yaki da Cututtuka masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum 14 da aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus. “Zuwa…

Hukumar Yaki da Cututtuka masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum 14 da aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus.

“Zuwa karfe 9.30 na daren 29 ga watan Maris, an samu jimillar mutane 111 da suka kamu da COVID-19 a Najeriya, inda mutum guda ya rasu”, inji hukumar a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Tara daga cikin sabbin kamun dai a Legas suke, biyar kuma a Yankin Babban Birnin Tarayya.

Yawan wadanda suka kamu da cutar a Legas ya karu zuwa 68, yayin da na Abuja suka kai 21.

Ga dai yadda adadin ko wacce jiha yake a halin yanzu:

Alkaluma: Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta najeriya (NCDC)