✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Gwamnatin Filato ta rufe iyakokin jihar

A kokarin da gwamnatin Jihar Filato take yi na kare yaduwar cutar  coronavirus a jihar, za ta hana zirga-zirga a jihar ta hanyar rufe dukkan…

A kokarin da gwamnatin Jihar Filato take yi na kare yaduwar cutar  coronavirus a jihar, za ta hana zirga-zirga a jihar ta hanyar rufe dukkan hanyoyin da ke shiga jihar, tun daga ranar Lahadi da karfe 6 na yamma zuwa karfe 7 na safiyar ranar Litinin.

Domin hana matafiya daga wasu jihohin shigowa jihar, har sai yadda hali ya yi. Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Danladi Abok Atu ne ya bayyana haka, a wani taron manema labarai da ya kira a gidan gwamnatin jihar, da ke garin Jos a ranar Asabar.

Ya ce, za a rufe hanyoyin da ke kan iyakokin shigowa jihar ne, don ganin an hana shigowar matafiya daga wasu jihohi zuwa jihar da hana zirga-zirgar jama’a a cikin jihar, a kokarin hana bullar cikin jihar .

Farfesa Danladi Atu, ya yi bayanin cewa a karin sababbin matakan da aka dauka, kan wannan al’amari, daga yanzu masu Keke Napap zasu rika daukar fasinja mutum daya ne a jihar, haka kuma masu kananan motocin haya za su rika daukar fasinjoji mutu hudu ne, duk da direba.

Ya ce, tuni gwamnatin jihar ta kafa wata gidauniya, wadda zata rika neman taimako daga kamfanoni da sauran jama’a masu hali, don ganin an tallafawa jama’a kan halin da za a shiga, sakamakon wannan al’amari.

A kokarin gwamnatin jihar na ganin ta kare bullar wannan annoba, tuni ta rufe kasuwanni da haramta bukukuwa da hana taruwar mutane fiye da 50, a garin Jos da kewaye.

Ya yi kira ga al’ummar jihar su ci gaba da bada goyan baya da hadin kai, kan kokarin da ake yi na ganin an kare rayukan al’umma.