✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: Yadda wasu masallatai suka bijire a Jos

Wasu masallatan Juma’a sun bijire wa umarnin da hukumomi suka bayar na hana taruwar dimbin jama’a don kauce wa yiwuwar yaduwar cutar Coronavirus. A lokacin…

Wasu masallatan Juma’a sun bijire wa umarnin da hukumomi suka bayar na hana taruwar dimbin jama’a don kauce wa yiwuwar yaduwar cutar Coronavirus.

A lokacin da wakilinmu ya isa masallacin Juma’a na ‘Yan Taya da ke garin na Jos da misalin karfe 12 na rana ya ganewa idonsa yadda aka girke jami’an tsaro wadanda suka rika korar mutane.

Amma daga bisani kafin a tayar da salla jami’an tsaron suka janye. Kuma an yi sallar lafiya

Wakilin namu dai ya gano cewa dukkan masallatan Juma’a na Izala da ke bangaren Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir a garin na Jos sun gudanar sallar.

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir

Amma ba a gudanar da sallar ba a Babban Masallacin Juma’a na Jos da ke ‘Yan Dankali da wasu masallatai da dama a garin.

A yammacin ranar Alhamis ne Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Filato, Mista Dan Manjang, ya fitar da wata sanarwa da ke cewa gwamnati ba ta hana sallah a masallatai ba, amma kada su mutane su wuce 50.

A wasu jihohin Najeriya dai hukumomi sun ba da umarnin a hakura da tarukan ibada, musamman a inda za a tara mutanen da suka haura 50.