Yarima Charles mai jiran gadon Masarautar Birtaniya ya sake kamuwa da cutar Coronavirus har ma ya killace kan sa, a cewar fadarsa ta Clearance House cikin wani sako da ta wallafa a Twitter.
An sanar da labarin kamuwar tasa ne jim kadan kafin ya fita zuwa Winchester don halartar wani biki.
- Wanne ya fi tsakanin biyan kudin haya a wata da a shekara?
- Na biya Ladin Cima N40,000 a fim din Gidan Badamasi —Nazir Salihi
Sanarwar ta ce Yariman yana takaicin rashin samun damar halartar taron bikin da zai gudana a Winchester, lamarin da zai sa a sake shirya wata ziyarar da zarar ya samu waraka.
A ranar Laraba yariman da matarsa Camilla sun gaisa da mutane a wurin wata liyafa a gidan ajiye kayan tarihi na British Museum.
A ranar Alhamis gwaji ya nuna Camilla ba ta dauke da cutar. Wannan ne karo na biyu da Yarima Charles ya kamu da cutar.
A watan Maris na 2020 ne yariman mai shekara 73 ya fara harbuwa da cutar.
Ko a wancan lokaci, Fadar Buckingham ta ce Sarauniya Elizabeth na cikin koshin lafiya.