Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC, ta sanar cewa a ranar Lahadi, an samu mutum 57 sabbin kamuwa da cutar Coronavirus a fadin Najeriya.
Sanarwar hakan na dauke ne a taskar bayanai mai dauke da alkaluman Hukumar a shafinta na yanar gizo.
- ‘Kwadayi da son kai sun rufe idanun ’yan siyasa a Najeriya’
- ‘Kwankwaso ya bar mana bashin Naira biliyan 54 na ’yan kwangila’
Alkaluman sun nuna cewa, an samu mutum 20 sabbin kamuwa da cutar a birnin Tarayya Abuja, sai Legas mai mutum 19 da Bayelsa mai mutum bakwai.
Sauran jihohin da aka samu sabbin kamuwar sun hada Kaduna mai mutum 7, Ribas da Osun mutum uku-uku, sai kuma Jigawa da mutum daya.
Ya zuwa yanzu, jimillar wadanda cutar ta harba a fadin kasar tun bayan bullarta karon farko a watan Fabrairun bara sun kai 163,793.
Haka kuma daga ciki mutum 154,107 sun warke, yayin da kuma mutum 2,060 suka riga mu gidan gaskiya.