Akalla mutum 39 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon annobar Coronavirus a birnin Shanghai na China mai hada-hada a ranar Asabar.
BBC ya ruwaito cewa wannan shi ne adadi mafi yawa da aka samu tun tsaurara dokar kulle makonni hudu da suka gabata.
- Mece ce gaskiyar matsalar ‘Dannau’ a mahangar likitanci?
- Cutar Ebola ta sake bulla a Dimokuradiyyar Kongo
A ranar Litinin da ta gabata aka ba da rahoton mutum na farko da ya mutu tun sake dawowar annobar, da kuma samun dubbai da suka kamu a rana guda.
Birnin Shanghai mai al’umma miliyan 25 yanzu haka na fama da barkewar wannan annoba mafi girma a China kawo yanzu.
Ana ci gaba da daukar matakai masu tsauri, da kwashe mutane daga gidajensu domin yi feshi.
Sannan a Beijing, jami’ai na gargadi kan barazanar da cutar da ke yaduwa cikin gaggawa ke haifarwa.