✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus ta kashe karin mutum 18 a Najeriya

Yanzu jimillar adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya daga zuwa 2,117.

An samu karin mutum 18 da suka mutu sakamakon cutar Coronavirus a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin alkaluman da Hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar ta fitar a yammacin ranar Alhamis.

Yanzu jimillar adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya daga zuwa 2,117 tun bayan bullarta karon farko watan Fabrairun bara.

Kazalika, alkaluman da NCDC ta fitar sun nuna an samu karin mutum 122 sabbin kamuwa da cutar a Jihohi 9 na kasar da suka hada da Legas (105), Imo (4), Kaduna (40, Akwa Ibom (3), Abuja (2), Delta (1), Ribas (1), Oyo (1) da kuma Ekiti(1).

Ya zuwa yanzu, jimillar mutum 166,682 ne suka kamu da cutar da kuma adadin mutum 162,521 da suka warke.

%d bloggers like this: