✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus ta kashe karin mutum 16 a Najeriya — NCDC

A ranar Alhamis, an samu karin mutum 16 da suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus. Sabbin alkaluman da Hukumar Dakile…

A ranar Alhamis, an samu karin mutum 16 da suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus.

Sabbin alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren jiya na Alhamis, sun nuna an kamu samu karin mutum 877 sabbin kamuwa da cutar a wasu jihohin kasar.

Sabbin mutum 877 da suka kamu a jihohi 26 na kasar ciki har da birnin Abuja sun hadar da; Legas – 273, Kaduna – 87, Ribas – 58, Akwa Ibom – 47, Ebonyi – 47 Ogun – 46, Abiya – 34, Imo – 34, Kano – 34, Oyo – 26, da Osun – 22.

Sauran su ne; Gombe – 20, Ekiti – 19, Kuros Riba – 15, Abuja – 15, Filato – 11, Enugu – 9, Kebbi – 8, Borno – 7,  Neja – 6, Bayelsa – 5, Nasarawa – 4, Kwara – 2, Katsina – 1, da Sakkwato – 1.

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna an samu jimillar mutum 150,246 da suka kamu sannan kuma akwai jimillar mutum 1,803 da suka mutu tun bayan bullar cutar a kasar.