An samu karin mutum 747 da suka kamu da cutar Coronavirus a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne cikin alkaluman da Hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar ta fitar a yammacin ranar Laraba.
Alkaluman da NCDC ta fitar sun nuna karin mutum 747 sabbin kamuwa da cutar sun fito daga Jihohi 14 ciki har da Abuja, babban birnin kasar.
Ga jerin jihohin da aka samu sabbin kamuwar a ranar Laraba:
- Legas-488
- Akwa Ibom-121
- Oyo-29
- Rivers-25
- Ogun-15
- Abuja -13
- Kaduna-13
- Kwara-11
- Ekiti-10
- Osun-10
- Edo-6
- Abiya-3
- Anambra-2
- Filato-1
Ya zuwa yanzu, jimillar mutum 176,011 aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma adadin mutum 165,208 da suka warke.
Alkaluman NCDC sun nuna jimillar adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya daga zuwa 2,167 tun bayan bullarta karon farko watan Fabrairun bara.
A baya-bayan nan ne aka samu bullar sabon nau’in cutar korona da ake kira Delta a kasar wanda masana ke cewa yana da saurin yaduwa matuka.