Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa a ranar Laraba an samu mutum 195 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus.
Da wannan sabon lissafin ne hukumar ta nuna cewa zuwa tsakar daren 6 ga watan Mayu, “mutum 3,145 ne aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.
Daga cikin wadannan mutum 195 da aka tabbatar sun kamu a baya-bayan nan dai, 82 a jihar Legas suke, sai 30 a Kano, 19 a Zamfara, 18 Sakkwato, 10 a Borno, tara a Yankin Babban Birnin Tarayya.
Akwai kuma takwas a jihar Oyo, biyar a jihohin Kebbi da Gombe, hudu a Ogun, uku a Katsina, sai jihohin Ogun da Adamawa da ke da mutum guda guda da suka kamu.
Hukumar ta NCDC ta kara da cewa daga cikin adadin wadanda suka kamu an sallami mutum 534 bayan sun warke, yayin da mutum 103 suka riga mu gidan gaskiya.
Kididdigar da NCDC ta fitar ta nuna cewa har yanzu jihar Legas ce kan gaba a yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da mutum 1,308, sai jihar Kano mai mutum 427 sai kuma Yankin Babban Birnin Tarayya mai mutum 316.