An samu karin mutum 19 da suka rasa rayukansu sakamakon cutar Coronavirus a wasu jihohi 12 da ke fadin Najeriya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito hakan na kunshe cikin alkaluman da Hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar ta fitar a ranar Juma’a.
- An tura tawagar bincike ta musamman kan kisan matafiya a Jos
- Girgizar kasa ta kashe mutane 300 a Kasar Haiti
Yanzu jimillar adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya daga zuwa 2,721 tun bayan bullarta karon farko watan Fabrairun bara.
Kazalika, alkaluman da NCDC ta fitar sun nuna an samu karin mutum 281 sabbin kamuwa da cutar cikin awa 24 da suka gabata a jihohi 12 da kuma Abuja, inda aka samu mutum 111.
Jihohin da aka samu sabbin kamuwar sun hada da Legas (34), Edo (33), Kwara (20), Filato (20), Ribas (17), Abia (10), Imo (8), Delta (7), Nasarawa (7), Akwa Ibom (3) da kuma Oyo (2).
Ya zuwa yanzu, jimillar mutum 205,779 ne suka kamu da cutar da kuma adadin mutum 193,631 da suka warke.