✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Gwamnati na bibiyar mutum sama da 4,000

Gwamnatin Najeriya ta ce tana bibiyar dubban mutane a fafutukar da take yi ta hana cutar Coronavirus yaduwa. Ministan Yada Labarai da Al’adu Alhaji Lai…

Gwamnatin Najeriya ta ce tana bibiyar dubban mutane a fafutukar da take yi ta hana cutar Coronavirus yaduwa.

Ministan Yada Labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammed ne ya fadi haka yayin da yake jawabi ga manema labarai game da inda aka kwana a yakin da ake yi da cutar.

“Akwai mutum 4,370 da muke bibiya”, inji shi.

Sai dai kuma a cewarsa yin hakan abu ne mai cike da kalubale, kasancewar wasu ’yan Najeriyar da suka dawo daga waje adireshi da lambobin waya na bogi suka bayar, lamarin da ya sa ake shan wahala wajen gano inda suke.

Ministan ya kuma ce gwamnati ba ta samun irin goyon bayan da ake bukata a lokaci irin wannan daga ’yan kasar.

“Da dama sun shagaltu da suka mara ma’ana a maimakon su bi umarnin da aka bayar don kare lafiyar jama’a”, inji shi.

Daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka don hana cutar yaduwa dai har da rufe hanyoyin shigowar kasar ta sama da ta kasa da rufe makarantu, da kuma umarni ga kananan ma’aikata su yi aiki daga gida.