✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: China ta dage dokar killace kai

Matakin ya kawo karshen tsare-tsaren Gwamnatin China na yaki da annobar Coronavirus.

A karon farko cikin shekaru kusan uku, China ta dage dokokin killace kai saboda Coronavirus ga bakin da suka isa kasar daga wasu kasashen.

Matakin ya kawo karshen tsare-tsaren Gwamnatin China na yaki da annobar Coronavirus.

Sai dai rahotonni na cewa har yanzu dokar da ta bukaci matafiyi ya nuna shaidar ba ya dauke da cutar kafin isa kasar na nan daram.

Sauyin na ba-zata da aka yi ya janyo karuwar mutanen da suka kamu da cutar har wasu kasashen suka kakaba wa matafiya daga China takunkumi.

China dai ta bayyana matakan da kasashen ke dauka a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.

A baya-bayan nan ne Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi gargadin cewa China na nuku–nuku tare da boye ainihin tasirin da annobar Coronavirus ta yi wa kasar – musamman ma alkaluman wadanda suka mutu.

Darektan Bayar da Agajin Gaggawa na hukumar, Dr Michael Ryan, ya ce abin da suke gani a China kan cutar Coronavirus ba shi ne ainihin abin da yake faruwa ba musamman idan aka duba wadanda ake kwantar wa a asibiti da ke bukatar kulawar gaggawa da kuma wadanda ke mutuwa sanadin cutar.