✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus ba ta kama ni ba —Ahmed Musa

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya, Ahmed Musa, ya musanta labarin da ke wadari a kafafen sadarwa na zamani cewa ya…

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya, Ahmed Musa, ya musanta labarin da ke wadari a kafafen sadarwa na zamani cewa ya kamu da cutar coronavirus.

Ahmed Musa ya karyata labarin ne, wanda ya kira labaran bogi, a shafinsa na Twitter.

“Ku yi watsi da duk wani labarin karya da cewa ni ko iyalina mun kamu da cutar COVID-19.

“Mun dai killace kanmu na tsawon mako biyu kasancewar ba mu jima da shigowa ba daga Saudi Arebiya”, inji Ahmed Musa, wanda ke wasa a kungiyar kwallon kafa ta Al-Nasr da ke Saudi Arebiya.

Ya kuma mayar da martini ga wani sakon Twitter (wanda aka cire daga bisani) da ke ambato shi yana cewa ya kamu: “Cire wannan labarin bogin don Allah”.

Dan wasan ya kuma yi kira ga masu bibiyar sa a shafin na Twitter da su bi tsarin nisa da juna su kuma kaurace wa labarin bogi.