Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum goma wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19.
Wannan bayani yana zuwa ne dai jim kadan bayan sanar da samun karin mutum 11 da suka warke aka kuma sallame su a jihar Legas.
“An ba da rahoton samun sabbin wadanda suka kamu da COVID-19 a Najeriya; bakwai a Legas, uku kuma a Yankin Babban Birnin Tarayya”, inji NCDC a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Ta kuma kara da cewa, “Zuwa karfe 8.00 na daren 2 ga watan Afrilu, akwai mutum 184 da aka tabbatar sun kamu da cutar. Daga cikinsu an sallami mutum 20 yayin da wasu mutum suka rasu”.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC da maraicen Alhamis, Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce an fara ganin alamun yada cutar daga wannan al’umma zuwa waccan.
Don haka, a cewar shi, “Dokar hana fita a jihohin Legas da Ogun da Yankin Babban Birnin Tarayya zai taimaka yayin muke kara zage dantse don ganowa da tabbatar da masu dauke da COVID-19”.