Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana dokar hana fita a garuruwan Gumel da Birnin Kudu da kuma Gujungu bayan da aka samu wasu mutum biyu sun kamu da cutar coronavirus.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne ya fadi haka yayin wani taron manema labarai da ya kira ranar Talata.
Gwamnan ya ce dokar rufe garuruwan za ta fara aiki ne daga karfe 12 na daren Alhamis domin a bai wa jama’a damar tanadin kayan abinci saboda azumi.
- Coronavirus: Jigawa ta karbi almajirai 524 daga Kano
- Dokar hana fita: Yadda rayuwar wasu ta kuntata a Jigawa
Da ya juya ga batun karamar hukumar Kazaure inda aka ayyana dokar hana fita makwanni biyu da suka gabata, Gwamna Badaru ya ce daga cikin mutane 17 da ake zargin suna dauke da cutar saboda hulda da suka yi da wanda ya kamu na farko, 16 ba su da ita, yayin da ake jiran sakamakon gwajin mutum na 17.
A cewar gwamnan, da zarar an samu duka mutum 17 ba su da ita za a janye dokar.
Ya kuma jaddada matsayinsa na cewa duk da gwamnonin jihohi sun yanke shawarar mayar da almajirai garuruwa ko jihohi ko kasashensu na asali, gwamnatin Jigawa ba za ta dauki wannan mataki ba.
Gwamnan ya ce ko da zai kori almajirai to sai an ga bayan annobar coronavirus.