An killace Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia bayan ya harbu da cutar coronavirus.
Ikpeazu ya killace kansa ne tun bayan fitowar sakamakon gwajin da ya tabbatar da ya kamu da cutar coronavirus, a cewar Kwamishinan Yada Labaran jihar John Okiyi Kalu.
Ya ce gwamnan ya kuma mika ragamar mulkin jihar ta Abia ga mataimakinsa, Rt Hon Ude Oko Chukwu, har sai abin da hali ya yi.
Sanarwar ta ce bayan sakamakon gwajin farko da aka yi masa ya nuna ba shi da ita, gwamnan ya sake mika kansa ga hukumar NCDC ta sake masa gwajin cutar.
Sai dai kuma sakamakon gwajin na biyu ya nuna gwamnan ya harbu da cutar.
Sanarwar ta ce Ikpeazu wanda likitoci ke ci gaba da duba lafiyarsa ya bukaci jama’ar jihar da su bayar da muhimmanci ga yakin da ake yi da COVID-19, duk da yake ba lallai ne cutar ta yi kisa ba.
Tun da farko a ranar 30 ga watan Mayu Ikpeazu ya mika kansa a yi masa gwajin cutar coronavirus, kana ya umurci da a yi wa dukkan ‘yan Majalisar Zartaswar Jihar gwajin.
A wancan karon sakamakon gwajin ya nuna gwamnan ba shi da cutar, lamarin da ya sa ya bukaci gwaji na biyu domin sake tabbatarwa.