An kawo karshen saka takunkumi da nuna takardar shaidar karbar allurar rigakafin Covid-19 a Faransa, matakin da gwamnatin kasar ta dauka a ranar Litinin.
Wannan mataki dai ya nuna cewa ga dukkan alamu Faransawa sun yi na’am da shi na kara tabbatar da cewa ana gab da shawo kan annobar kamar yadda Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito.
Wannan matakin na nufin cewa Faransawa da ke bukatar zuwa gidajen cin abinci ko kuma gidan kallo ko kuma shakatawa, hadi da wuraren baje koli, suna da damar zuwa ba tare da wata tsangawa ba.
Haka zalika babu batun amsa tambayar rashin dalilin sanya takunkumi a makarantu, ko a katafaren kantuna, wanda hakan ke nufin jama’a za su gudanar da harkokin su ba kamar yadda aka saba ba kafin lokacin dokar kulle.
Amma gwamnati yanzu haka ta tabbatar da cewa wuraren da ake samun cunkoson jama’a, misali motocin safa, da asibitoci ya zama wajibi mutane su kare kai, tare da baiwa kamafanoni masu zaman kan su zabi, ko su ci gaba da amfani da dokar Covid-19 din ko kuma su kyale jama’a haka nan.
An samu raguwar labarin catar Covid-19 sakamakon yakin da ke wakana tsakanin kasashen Rasha da kuma Ukraine, a gefe guda kuma batun takarar shugabancin kasar Faransa, inda masana ke ganin cewa annobar da ta kawo tsaiko a bangarori da dama a duniya ta yi nisa sosai.
A zahiri, bayan makonni da samun raguwar yaduwar cutar, hukumomin lafiya a Faransa sun ce adadin sabbin cututtukan sun haura 73,000 a ranar Juma’a, kadai daga 60,000 a mako daya da ya wuce.
Abin da kwararru ke cewa har yanzu shi ne, gwamnati kuma ta gaza cim ma burinta na kawo karshen adadin marasa lafiya da ake jibgewa a sashen ba da agajin gaggawa ko kuma killacewa kasa da 1,500.