✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Abin da ya sa muka bijirewa dokar Legas- Izala

Kungiyar Izalatul bidi’a wa’ika’matus Sunna mai Hedikwata a  Jos reshen jihar Legas ta bayyana dalilan da ya sa ba tabi umarnin gwamnatin Legas ba na…

Kungiyar Izalatul bidi’a wa’ika’matus Sunna mai Hedikwata a  Jos reshen jihar Legas ta bayyana dalilan da ya sa ba tabi umarnin gwamnatin Legas ba na dakatar da Sallar juma’a a daukacin masallatan ta a jihar ba.

Cikin masallacin

Jagoran kungiyar a Legas Shaikh Dalhatu Abubakar, ya shaida wa Aminiya cewa gwamnatin Legas bata sanar masu a hukunce ba, ya ce basu ga dalilan da zai sanya su dakatar da Sallar Juma’a ba, dan haka ne suka umarci mabiyansu suyi Sallar juma’a a daukacin masallatansu da ke jihar.

Shaikh Dalha, ya ce kamata ya yi gwamnati tayi zama da masu ruwa da tsaki a harkar addinai a karkashin kungiyoyin daban-daban sannan ta nemi shawararsu hanyoyin magance annoba a addinance.

“Ba mu sami sakon gwamnati na dakatar da sallah a hukumance ba, dan haka muka yi salollinmu, mun yi lafiya mun kare lafiya, muna fatan Allah ya ye mana wannan musifa ta coronavirus.” inji shi.

A kasuwar mile 12 ma masallatai da dama sun gudanar da Sallar juma’a ba tare da amfani da na’urar amsa kuwa ba.

Gwamnatocin jihohin Legas da Ogun sun bada umarnin dakatar da taron da ya haura na mutum 50 a wuraren ibada, sai dai a jihar Ogun umarnin bai yi tasiri ba, domin masallatan juma’a da dama sun yi salollinsu kamar yadda aka saba.

Lokacin da ake huduba