Sabon kocin Tottenham, Antonio Conte ya fara jan ragamar kungiyar da kafar dama, bayan da ya samu nasara a wasan farko da kungiyar ta fafata karkashin jagorancinsa.
Tottenham ta samu nasarar lallasa Vitesse da kwallaye 3-2 a wasan farko da Conte ya jagoranci kungiyar a gasar Europa League a daren ranar Alhamis.
- An harbe mai garkuwa da mutane a wurin karbar kudin fansa
- An kashe mutum 3 a rikicin ’yan sanda da masu Keke Napep a Legas
Ana iya tuna cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ce Tottenham ta sanar daukar Antonio Conte a matsayin sabon kocinta da ya maye gurbin wanda ta kora, Nuno Espirito.
Farawa da kafar dama da Conte ya yi na zuwa ne yayin da a mintuna 45 na farkon wasan magoya bayan Tottenham suka yi masa tsayuwar ban girma ganin yadda cikin mintuna 28 kungiyar tasa da ke wasa a gida ta samu nasarar jefa kwallaye 3 rigis a ragar Vitesse.
A shekarar 2016 dai Antonio Conte ya samu nasara a wasan farko da ya jagoranci kungiyar Chelsea, daga bisani kuma ya samu nasara lashe wasanni 13 a jere.
Haka kuma a waccan lokacin kungiyar ta Tottenham da a yanzu yake horaswa ce ta kawo karshen nasarorin da ya jera inda ta doke Chelsea da kwallaye 2-0.