Ganin irin matsanancin halin da ake ciki na dokar hana fita da aka kafa a jihohin Najeriya, don dakile yaduwar annobar coronavirus da kuma shigowar azumin watan Ramadan.
Cocin Assemblies of God ta kasa, ta gundumar Saminaka da ke Jihar Kaduna, ta tallafawa al’ummar Musulmi da Kirista na yankin, sama da mutum 100, da kayayyakin abinci. Tare da wayar masu da kai, kan matakan kare yaduwar wannan annoba a garin Saminaka.
Kayayyakin abincin da cocin ta raba, sun hada da: shinkafa da masara da dawa da taliya.
Da yake jawabi a wajen raba kayan tallafin Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani, ya yabawa shugaban cocin na gundumar Saminaka.
Ya ce, wannan tallafi da shugaban cocin ya yi, abin koyi ne ga dukkan al’umma, musamman a wannan lokaci da ake ciki. Don haka ya yi addu’ar Allah Ya saka masa da alheri.
Sarkin wanda Wazirin Saminaka Alhaji Muhammad Rabi’u Umar, ya wakilta ya yi kira ga al’ummar yankin, su rika bin dukkan shawarwarin da jami’an kiwon lafiya, suke bayarwa kan matakan kare yaduwar wannan annoba ta coronavirus, domin kare kansu da al’umma baki daya.
- Arida ta tallafawa marayu da talakawa 3,000 abinci a Kaduna
- An bukaci masu hali da su tallafawa talakawa
Tun da farko a nasa jawabin shugaban Cocin na ‘Assemblies Of God’ na Gundumar Saminaka, kuma wakilin shugaban cocin na kasa, a shiyyar jihohin Arewa ta Yamma, Rebaran Haruna Tutu, ya bayyana cewa babban abin da ya karfafa masa gwiwar raba wannan tallafi na kayayyakin abinci, ga al’ummar Musulmi da Kirista, shi ne domin sauke wani nauyi da Allah Ya dorawa duk wani shugaba, na tallafawa al’ummar da yake shugabanta.
Har’ila yau ya ce, ganin yanayin da ake ciki na zaman kulle sakamakon wannan annoba, da kuma shigowar azumin wata Ramadan. Suka yanke shawarar su tallafawa al’ummar Musulmi da Kirista baki daya da kayayyakin abinci.
Rebaran Haruna, ya ce wadannan mutane da suka tallafawa da kayayyakin abinci da suka hada da, shinkafa da masara da dawa da taliya sun kai mutum 100.
‘’Jin dadin zaman lafiya da muke da shi, da son ci gaban wannan zaman lafiya, ya dada karfafa mana gwiwar bayar da wannan tallafin kayayyakin abinci, ga al’ummarmu. Domin mu nunawa duniya, cewa mu Kirista da Musulmi muna zaune lafiya a wannan yanki.’’
Rebaran Tutu, ya yi bayanin cewa duk wanda Allah Ya bashi damar da zai taimakawa wani, ya yi kokari ya yi wannan taimako, domin wannan wani nauyi ne da Allah Ya dora mana baki daya.
Ya ce, yin haka zai dada kawo zaman lafiya musamman a wannan lokaci da ake ciki, na wannan annoba ta coronavirus da kuma watan azumi.
Sannan ya yi kira ga gwamnatoci da malamai da fastoci da sauran al’umma, kowa ya ci gaba da kokari da addu’o’in Allah Ya kawo mana karshen wannan annoba ta Coronavirus.