✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ciwon mafitsara ya ci gaba da kwantar da Pele a asibiti

Zai ci gaba da kasancewa a asibiti a birnin Sao Paulo sakamakon sanyin mafitsara.

Shahararren dan wasan kwallon kafar nan dan kasar Brazil, Pele, zai ci gaba da kasancewa a asibiti a birnin Sao Paulo sakamakon sanyin mafitsara.

Cikin bayanan da Hukumomin asibitin suka bayyana a ranar Litinin sun ce da farko an kwantar da shi inda ake masa maganin sankarar hanji.

An dai kwantar da tsohon dan wasan mai shekaru 81, wanda ake wa inkiya da ‘O Rei’, wato sarki a asibin Albert Einstein na birnin Sao Paulo ne a ranar 13 ga watan Fabrairu don ci gaba da yi masa maganin lalurar hanji da yake fama da ita, wadda aka gano a watan Satumban shekarar da ta gabata.

Kwanaki takwas bayan an kwantar da shi ne likitoci suka ce sun gano sanyin mafitsara a tattare da shi, lamarin da zai tsawaita zamansa a asibitin.

Wannan ne lalurar rashin lafiya ta baya bayan nan da ta addabi tsohon dan wasan mai yawan shekaru, wanda bayyanarsa a bainar jama’a yake ci gaba da raguwa.

Dan wasan da ake ganin babu irinsa a duniya, wanda ainihin sunansa Edson Arantes do Nascimento, shi ne dan wasa daya da ya taba lashe kofunan duniya har uku.