Shahararren dan wasan kwallon kafar nan dan kasar Brazil, Pele, zai ci gaba da kasancewa a asibiti a birnin Sao Paulo sakamakon sanyin mafitsara.
Cikin bayanan da Hukumomin asibitin suka bayyana a ranar Litinin sun ce da farko an kwantar da shi inda ake masa maganin sankarar hanji.
- Mun bai wa gwamnati da ASUU wa’adin mako daya su sulhunta —Kungiyar Dalibai
- Rikicin Ukraine: Farashin mai ya tashi a kasuwar duniya
An dai kwantar da tsohon dan wasan mai shekaru 81, wanda ake wa inkiya da ‘O Rei’, wato sarki a asibin Albert Einstein na birnin Sao Paulo ne a ranar 13 ga watan Fabrairu don ci gaba da yi masa maganin lalurar hanji da yake fama da ita, wadda aka gano a watan Satumban shekarar da ta gabata.
Kwanaki takwas bayan an kwantar da shi ne likitoci suka ce sun gano sanyin mafitsara a tattare da shi, lamarin da zai tsawaita zamansa a asibitin.
Wannan ne lalurar rashin lafiya ta baya bayan nan da ta addabi tsohon dan wasan mai yawan shekaru, wanda bayyanarsa a bainar jama’a yake ci gaba da raguwa.
Dan wasan da ake ganin babu irinsa a duniya, wanda ainihin sunansa Edson Arantes do Nascimento, shi ne dan wasa daya da ya taba lashe kofunan duniya har uku.