✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ciwon baya

Tambayata ita ce; ni dai wani matsananci ciwon baya ne ke damuna  musamman idan na zo kwanciya. Shi ne nake so likita ya yi min…

Tambayata ita ce; ni dai wani matsananci ciwon baya ne ke damuna  musamman idan na zo kwanciya. Shi ne nake so likita ya yi min bayani a kan yadda zan yi na rabu da wannan matsalar.
Daga Fadima Duka-Wuya, Kano
Amsa: Kafin mu san mene ne ciwon baya da yadda yake aukuwa, ya kamata mu san ya shi gadon bayan yake. Gadon baya ya hada da sandar kasusuwan baya, da wasu faifaye ko kushin din da suke tsakankanin su kasusuwan, sai kuma naman da ya lullube shi da kuma jijiyar laka ta gadon baya da ke cikin shi sandar kashin.
Dukkanin wadannan abubuwa da aka lissafa wato da lakar, da kashin da tsokar da kushin din za su iya jin ciwo su sa ciwon baya. Kuma ana jin ciwon ne a tsakiyar baya daga kasan hakarkari zuwa kugu, domin duk zafin da aka ji a gefe ko kwibin wannan wuri ba sunanshi ciwon baya ba, watakil koda ce ko wani abin daban.
Ciwon baya ba karamar matsala ba ce, domin a kullum sai an je asibiti a kanta. Kusan an kiyasta cewa kowane mahaluki zai samu (ko ma ya taba samun) ciwon baya ko da sau daya ne a rayuwa, a wasu da dama kuma ya zauna ya ki tafiya. Mukan samu ciwon baya ne yayin da muka dauki abu mai nauyi, ko muka buge, ko muka murda bayan da karfi ba tare da mun sani ba, kamar a fagen wasanni ko wata cuta ta taba shi.
Abubuwan da kan kawo ciwon baya sun hada da:
1. Yawan shekaru: Wato girma ko tsufa. Wannan shi ne kan gaba wajen kawo ciwon baya, domin da wuya yara su yi. An fi ganin ciwon baya a dattijawa da tsofaffi wadanda bayansu ya riga ya fara rauni, ko kasusuwan suka riga suka fara zaizayewa saboda karancin ma’adinai irinsu bitaman na rukunin D da Calcium. Don haka idan yawan shekaru ne ke kawowa mutum ciwon baya sai an hada da magungunan bitaman da motsa jiki ta hanyar gashi wato Physiotherapy kafin abin yayi sauki.
2. Sai kuma kiba: Wadda kan kara wa gadon bayan nauyi, ta yadda tsokar da kashin da kushin din duk za su kasa samun sakewa. Mai wannan matsalar idan ba rage kibar ya yi ba, ba zai daina samun matsalar ba komi magani.
3. Gado: Akwai kuma wadanda akan haifa da karkataccen kashin gadon baya, kamar kusumbi ko doro ko dai wani rashin daidaito na kashin bayan wanda kan iya sa yawan ciwon bayan. Shi wannan idan aka gano hakan ne, yawanci tiyata ake a mikar da lankwasar.
4. Yawan aiki a tsaye ko a rusune ko a zaune na tsawon lokuta, zai iya  sa tsokar jikin kashin ta gajiya. Kai a wasu lokutan ma irin wannan kan iya sankarar da baya na dan wani lokaci. Yawan motsa jiki kan iya magance ciwon baya a masu irin wannan matsala.
5. Yawan daga nauyi: Mutane masu aikin daga nauyi sun fi kowa  samun hadarin zamowar kushin din da ke tsakankanin kashin gadon baya. Idan mutum zai daga nauyi ko da ruwan wanka ne kada ya daga daga rusune, sai daga tsugune. Don haka ne ma kuma muke kira ga masu sa leburori aiki su rika bin ka’idojin aiki, ta hanyar basu kayan daukar nauyi na zamani da insorar lafiya ga wadannan
6. Buguwa ta hadari: Wadda zata iya kuje tsokar ko ta sa karayar kashin, ko ta sa kashin ya matse lakar, ko ta sa kushin-kushin din tsakankanin su zamo. Don haka idan mutum ya taba buguwa a baya yana cikin hadarin samun ciwon baya.
7. Tsayi: An tabbatar da cewa wadanda suke da tsayi sosai sun fi sauran mutane yawan samun ciwon baya. Don haka idan kina da tsayi sosai za ta iya kasancewa shi ne.
8. Ciwon Sanyin kashi: Ga mai ciwon sanyin kashi wanda ya fi kama yatsu da gabobin hannu ko na gwiwoyi, za a iya rashin dace ya tabo har gadon baya. Don haka ba abin mamaki bane mai ciwon sanyin kashi ya ji bayansa ya fara ciwo. A irin wannan magungunan sanyin kashin kan iya sawa na bayan ma ya lafa.
9. Yanayin Wurin Kwanciya: Da yake kwanciyar barcin dare na daukar lokaci mai tsawo a kowace rana, yanayin kwanciya kan iya sa ciwon baya. Mutumin da ke kwana kan tabarma ba daya yake da mai kwana kan katifa ba, kuma katifar ma kowa ya san hawa-hawa ce.
Gadon baya bai cika son kwanciya a wuri mai tauri da laushi sosai ba, ya fi son tsaka-tsaki, wato katifa maras tauri sosai, kuma maras laushi sosai. Da yake kin ce sai lokacin kwanciya kike samun ta’azzarar ciwon ya kamata ki nemi irin wannan. Idan yanzu katifarki mai laushi sosai ce, sai ki nemi wadda ba ta kaita laushi ba, idan kuma mai tauri ce sai a nemi wadda ta fi ta laushi, amma kada a dauki mai laushi sosai.
10. Ciwon TB: Ciwon tarin fuka na TB kan iya barin huhu ya tabo  kashin gadon baya. Bayan huhu dama wuri na biyu da aka fi ganin ciwon tarin fuka shine kan kashin gadon baya. Don haka ba abin mamaki bane mai tarin fuka ya ji ciwon baya. Ga mai tarin fuka wanda ke shan magani, duk lokacin day a ji ciwon baya kwana daya, kwana biyu ya ki tafiya dole ya je a duba bayan sosai. Ban da wannan kwayar cuta ta TB akwai wau kwayoyin cutar da kan iya biyo jini ma su kama kashin gadon baya.
11. Ciwon Daji: A lokuta da dama masu matsalar ciwon daji ko na ina ne kan samu ciwon baya, domin ciwon daji kan bi jini ya hau kan kasusuwa. Ciwon daji ko na mama ko na bakin mahaifa ko na hanji ko na huhu, ko na mafitsara duk sun fi tafiya kashin gadon baya.
12. Al’ada da samun juna biyu da karin mahaifa: a wasu mata su kuma lokutan al’ada ne kawai kan kawo musu ciwon baya maimakon ciwon mara ko na kugu. Samun juna biyu ma idan cikin ya haura watanni biyar zai iya danne kashin gadon baya a samu jin zafi.
karin mahaifa ma wato fibroid kan iya jawo irin wannan. Idan mutum na da ciwon baya matsananci, ya duba duk wadannan abubuwa da aka lissafa ya kasa gano dalili, kai ko da ya gano dalili, yana da kyau kuma ya ziyarci karamin asibiti inda za a duba shi a bashi magunguna. Idan abun bai tafi ba, in son samu ne a je babban asibiti kamar asibitin kashi, inda za a fara da masa hotunan baya na d-ray da ma na zamani irinsu MRI idan ta kama, da ma sauran gwaje-gwajen jini. A lokacin ne za a gano ainihin musabbabi matsalar kafin a zo maganar magunguna, a wasu lokutan ma maganar tiyata ce.