✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

City ta yi warkajami a gidan takwararta ta kauye a Firimiyar Ingila

Wannan shi ne karo na bakwai da Guradiola ya ci wasa a Old Trafford ta biyu.

Manchester City ta yi warkajami a ziyarar da ta kai gidan takwararta ta kauye Manchester United yayin wasan hamayya da suka fafata a wannan Lahadin.

An dai barje gumin ne a gaban ’yan kallo 73,502 a wasan da Paul Tierney ya yi alkalancinsa a Old Trafford, inda City ta nana wa United kwallaye uku rigis ba tare da an mayar mata da martani ba.

Erling Haaland ne ya fara cin kwallo a minti na 26 da fara tamaula, karon farko da City ta samu fenariti a Old Trafford a Firimiyar Ingila a karawa 27.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Haaland ya ƙara na biyu da ka a minti na 49 bayan Bernado Silva kwaso kwallon daga kusurwa.

Saura minti 10 a tashi daga karawar City ta zura kwallo na uku a raga ta hannun, Phil Foden, hakan ya tabbatar da maki uku ga ƙungiyar Etihad.

Kenan United ta yi rashin nasara biyar daga wasa 10 da fara kakar bana, karon farko da ta yi haka tun bayan 1986/87.

Wasa na 37 kenan da ba a cin Manchester City da zarar Rodri ya buga mata tamaula, rabon da ta yi rashin nasara a lig tare da ɗan ƙwallon a cikin fili tun Fabrairun 2023 da Tottenham ta yi nasara.

Wannan shi ne karo na bakwai da Guradiola ya ci wasa a Old Trafford ta biyu da ya doke da yawa a karawar waje, bayan Arsenal da ya ci karo takwas a Emirates.

Tun bayan da Guardiola ya karɓi aikin horar da City a 2016 ya hada maki 145 fiye da United, yana da 649 ita kuwa tana da 504.